Kasar Philipines ta bijire wa MDD
March 3, 2018Shugaba Rodrigo Duterte na kasar Philippines ya umurci jami'an 'yan sandan kasarsa da su bijire wa duk wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya da zai shigo kasar da sunan bincike saboda zarginsa na cewa ba za yi wa kasar adalci ba. Umarnin shugaban na Philipines ya bayar da shi ne yayin da wata jami'ar hukumar Majalisar Dinkin Duniyar ke shirin shiga kasar kan wasu zarge-zarge na take hakkin jama'a.
Jayayyar shugaban dai na da alaka ne da bincike kan hukunta dillalan miyagun kwayoyi su dubu hudu da aka yi a kasar galibinsu ta hanyar kisa a shekara ta 2016. Yayin wani jawabi ga manyan jami'an 'yan sandan kasar, Mr. Duterte ya ce zai amince da bincike na hakika amma ba sai an yanke shawara sannan a ce ana zuwa bincike ba, abin da ya ce ihu ne bayan hari.