Kasar Rasha ta gargadi Amirka kan Siriya
April 10, 2018![USA | UN-Sicherheitsrat - Vertreter Russlands und UK streiten über Fall Skripal](https://static.dw.com/image/43275090_800.webp)
Kasar Rasha ta gargadi Amirka dangane da illar da ke tattare da matakin soji da wasu kasashen yammacin duniya ke da niyar dauka a Siriya idan zargin da ake yi wa Bashar al-Assad na amfani da makami mai guba ya tabbata. Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Dubiya Wassily Nebensja ya bayyana yayin taron kwamitin tsaro cewar duk wani hari na Amirka zai mayar da hannu agogo baya a kokarin warware rikicin da ake yi a Siriya.
Sai dai kuma shugaba Trump ya bayana wa manaima labarai cewar ya na shirin yanke shawara kan matakin da zai dauka a kan gwamnatin Bashar al-Assad bayan da ya sake tattauna da shugaban Faransa Emmanuel Macron kan wannan batu, yana mai cewa ba zai lamunta da amfani da makamai masu guba a kan 'yan tawaye ba.
A cewar 'yan gwagwarmaya na kasar Siriya, an kashe mutane fiye da 150 kuma kusan duba sun ji rauni a harin da sojojin Siriya suka kai da guba a garin Duma a ranar Asabar.