1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi Rasha da kin bin umarnin kungiyar NATO

Zulaiha Abubakar
January 25, 2019

Babban magatakardar kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana cewar kasar Rasha ta karya yarjejeniyar mallakar makaman kare dangi yayin da Amirka ke cigaba da barazanar ficewa.

Belgien Brüssel NATO-Generalsekretär Jens Stoltenberg
Hoto: picture-alliance/AP Photo/V. Mayo

Cikin watan Oktobar shekarar da ta gabata ne dai, Shugaba Donald Trump na Amirka ya sanar da cewar kasar za ta yi watsi da yarjejeniyar makaman matukar Rasha ta ki bin umarnin kungiyar tsaron ta NATO kan sababbin makaman masu linzamin da ta kirkira.

Kungiyar ta NATO ta kara da cewar sababbin makaman kare dangin dai na da wuyar ganowa ta na'urori masu kwakwalwa sannan suna da nisan zangon da za su iya isa kowanne yanki a Turai cikin kankanin lokaci bayan kasancewar su cikin rukunin makamai irin na Nukiliya. Har ya zuwa wannan lokaci dai Rasha ta gaza kare kanta.