Kasar Siriya ta Kafa dokar sake gina kasa
May 25, 2018An kaddamar da wannan doka ne cikin watan Afirilun wannan shekara daidai lokacin da dakarun gwamnatin kasar ke aikin murkushe guraren da 'yan ta'addan suka yi kama a Damascus, shekaru bakwai bayan gumurzun da yayi sanadiyyar rasa rayukan dubban al'umma,
Gwamnati ta sanar da ba wa 'yan gudun hijira damar zuwa don nuna cikakkiyar shaidar mallakar dukiyoyinsu da suka gudu suka bari don hukuma ta biyasu: Sai dai a bangare guda kungiyoyin agaji sun bayyana shakku game da samun shaidar mallaka a gurin 'yan gudun hijira bayan irin yakin da aka dauki shekaru ana yi a kasar.
Da yake tofa albarkacin bakinsa game da wannan doka Firaministan kasar Labanon Saad al-Hariri, ya bayyana sabuwar dokar da barazana ga 'yan gudun hijira sama da miliyan daya da ke zaune a kasar don kada su koma kasarsu ta Siriya. Koda yake Shugaba Bashar Al-Assad na Siriya ya ce an yi wa dokar mummunar fahimta.