1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe 26 na cikin wadi na kangin bashi

Abdullahi Tanko Bala
October 14, 2024

Kasashe 26 mafiya talauci a duniya na cikin wadi na kangin bashi mafi muni cikin shekaru 18 da suka gabata a cewar wani sabon rahoto da bankin duniya ya fitar.

Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha
Addis Ababa, babban birnin kasar HabashaHoto: Joerg Boethling/IMAGO

Rahoton na bankin duniya  ya ce kasashen 26  suna cikin mawuyaci fiye da kowane lokaci tun shekaru 2006.

Kasashen sun hada da Afghanistan da Yemen da Koriya ta Arewa. Sauran kasashen suna yankin Afirka ne kudu da hamadar Sahara sun kuma hada da Habasha da Chadi.

A cewar Bankin duniyar kasashen sun fi fadawa talauci a yanzu fiye da yadda suke a lokacin annobar korona duk da cewa sauran kasashen duniya tattalin arzikinsu ya farfado