1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kasashe 52 na son MDD ta haramta wa Isra'ila sayen makamai

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 3, 2024

A cikin kasashen da suka sanya hannu a wasikar akwai Saudi Arebiya da Brazil da Algeria, sai China da Iran da kuma Rasha

Shugaban Türkiyya Recep Tayyip Erdogan
Hoto: DHA

Kasar Turkiyya ta mika wa Majalisar Dinkin Duniya wasikar bukatar haramta wa Isra'ila cinikin makamai, mai dauke da sa hannun kasashe 52 na duniya.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana hakan a kasar Djibouti, lokacin wani taro kan alaka da ke tsakanin Turkiyya da Afirka, yana mai ayyana masu sayar wa Isra'ila makaman a matsayin masu taimaka mata wajen aikata kisan kare dangi.

Karin bayani:Olaf Scholz na Jamus na ziyara a Turkiyya kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Daga cikin kasashen da suka sanya hannun wannan wasika akwai Saudi Arebiya da Brazil da Algeria, sai China da Iran da kuma Rasha.

Sai kuma kungiyar kasashen Larabawa ta Arab League da kuma ta hadin kan musulmi wato Organization of Islamic Cooperation.

Karin bayani:Erdogan ya nemi a kakaba wa Isra'ila takunkumi kan makamai

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kakaba wa Isra'ila takunkumin hana sayen makamai, a matsayin mafita tilo ta kawo karshen yakin Gaza.