Kasashe daga EU sun ki yarda da Maduro
February 4, 2019Goyon bayan kasashen Birtaniya da Faransa da Spain da Potugal da Sweden da Denmark da Ostiriya da Tarayyar Jamus da Holland na zuwa ne, bayan cikar wa'adin kwanaki takwas da aka debar wa gwamnatin Maduro na ya kira gudanar da sabon zabe a karshen makon da ya gabata.
Ana zargin shugaban na Venezuela da mulkin kama karya da karya tattalin arzikin wannan kasa da ke zama mamba a kungiyar kasashe masu albarkatun man fetur ta OPEC wadda ke da yawan al'umma miliyan talatin. Sai dai a na shi bangare Shugaba Maduro ya zargi masu fada a ji na Turai da kasancewa 'yan a bi yarima a sha kida ne na shugaban kasar Amirka Donald Trump.
A watan Janairun da ya gabata ne dai Guaido, wanda ke jagorantar majalisar Venezuela da 'yan adawa ke da rinjaye, ya ayyana kansa a matsayin shugaban rikon kwarya, batu da ya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin kasashen duniya, da haifar da zanga-zanga a titunan kasar. Firaministan Spain Pedro Sanchez ya ayyana goyon bayan kasarsa ga shugaban adawar bayan cikar wa'adin da aka debar wa Maduro.
Ita ma Faransa ta sakon da Shugaba Emmanuel Macron ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewar al'ummar Venezuela na da 'yancin walwala kamar yadda yake a kowace kasa da ake da tsarin mulki na dimukuradiyya. A kan haka ne ma ministan kula da harkokin wajen kasar Jean-Yves Le Drian ya jaddada dalilansu na daukar matakin goyon baya ga shugaban adawar ta Venezuela.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya Jeremy Hunt da shafinsa na sada zumunta ya nuna amannar kasar ga Guaido a matsayin shugaban gwamnatin riko, ya zuwa lokacin da za'a gudanar da zaben kasa. Ya kara da cewar wajibi ne a kawo karshen gwamnatin Maduro mara alkibla da madafa.
Rasha da China dai da suka zuba jari da bayar da rancen biliyoyin daloli a kasar ta Venezuela, na goyon bayan cigaban gwamnatin Maduro, a wani mataki na fadada sabanin da ke tsakaninsu da Amirka.
A martaninta a wannan Litinin, Rasha ta zargi kasashen na Turai da karambanin tsoma baki cikin matsalar wata kasa daga waje, tare da kira da a bar Venezuela ta sasanta rikicinta na cikin gida da kanta. Gwamnatin ta Maduro dai na biyan basukan da ta karba daga Rasha da China da albarkatun mai.