1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kasashe hudu na neman warware rikicin Sudan a Washington

Mouhamadou Awal Balarabe
October 24, 2025

Bangarorin da ke fada da juna a Sudan na haduwa da jami'an wasu kasashe hudu a Washington don neman bakin zaren warware rikicin da ke addabar kasar.

Kasashe da dama na shiga tsakani don sasanta  al-Burhane da Hamdan Daglo a Sudan
Kasashe da dama na shiga tsakani don sasanta al-Burhane da Hamdan Daglo a SudanHoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

Wakilai daga Amurka, Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar za su gana a Washington a yau Juma'a (24.10.2025) da bangarorin da ke fafatawa da juna a Sudan da nufin kawo karshen fada tsakanin bangarorin biyu.

Tun a watan da ya gabata ne, kasashen waje masu tasiri suka yi kira da a tsagaita wuta domin ba da damar kai agajin jin kai ga mabukata, sannan a tsagaita wuta gaba daya, wanda hakan zai share fagen mayar da Sudan kan tafarkin mulkin farar hula.

Karin bayani: Sudan ta Kudu: Yaushe za a samu zaman lafiya?

Wani babban jami'i da ke da kusanci da kasashen hudu ya shaida wa kanfanin dillancin labarai na AFP cewa taron na da niyar matsa lamba ga bangarorin biyu da ke fafatawa da su amince da tsagaita wuta na tsawon watanni uku, domin ba da damar shigar da agajin jin kai. Jami'in ya ce wakilan bangarorin za su gana da kasashen hudu a tarurruka biyu daban-daban.