1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kasashe masu karfin tattalin arziki na taro a Jamus

October 5, 2023

Kasashe mafi karfin tattalin arziki na duniya na taro a birnin Bonn na kasar Jamus domin bayyana matsaya kan kudaden da za su zuba wa babban Asusun kasa da kasa mai kula da sauyin yanayi.

Kasashe masu karfin tattalin arziki na taro a Jamus kan sauyin yanayi.Hoto: Dr Adefires Worku

Babba burin wannan Asusu da ake kira Green Climate shi ne tilasta wa kasashe masu ci gaban masana'antu biyan diyya ga kasashe matalauta da ke dandana radadin sauyin yanayi da kuma canja sheka izuwa amfanin makamashi mai tsafta wajen bunkasa tattalin arziki.

Karin bayani: Manufofin ci-gaba mai dorewa

Asusun dai na Green ya tanadi gudanar da tsare-tsare da ayyuka sama da 200 a matsayin tallafi musanman ma a nahiyar Afrika da Asiya da kuma Latin Amurka da kuma tsibirin Caraibes. 

Karin bayani: AU za ta samar da dala biliyan 26 domin yaki da sauyin yanayi

Sai dai yayin da gabanin buda taron kasashen Tarayyar Turai da Burtaniya da Kanada da kuma Koriya ta Kudu suka sanar da ba da biliyoyin daloli, har yanzu Amurka ba ta ce ufan ba a game da tallafin da take sa ran bayar wa.