1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Chadi ta bi sahun korar sojojin Faransa

Salissou Boukari LM
November 29, 2024

Yayin da kasar Chadi ta sanar da soke huldar soja tsakaninta da kasar Faransa, a daidai lokacin da Chadin ke neman karfafa hulda da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar.

Chadi | Shugaban Kasa | Mahamat Idriss Deby | Alaka | Faransa | Nijar
Shugaban ksar Chadi Mahamat Idriss Deby Hoto: Israel Matene/REUTERS

Ministan harkokin waje na Chadin da ke zaman kusan kasa ta karshe a yankin Sahel da sojojin Faransa ke cikinta Abderaman Koulamallah ya sanar da cewa, kasar ta kawo karshen yarjejeniyar tsaro da aka kulla tsakaninta da Faransa sa'o'i kalilan bayan ziyarar da shugaban diflomasiyyar Faransan Jean-Noel Barrot ya kai Chadin. Sanin kowa ne dai Chadi ce cikakkiyar damar da Faransa ke da ita ta kasancewa a yankin Sahel, duk kuwa da cewa kasashen yankin kamar Nijar da Mali da Burkina Faso da ke a matsayin aminanta sun raba kaya da uwar gijiyar ta su da ta yi musu mulkin mallaka wato Faransa. Sai dai kuma a baya-bayan nan an ga  Chadin ta hanyar gwamnonin yankin iyakar kasashen biyu na jaddada aniyar aiki tare, lamarin da ke nuni da cewa akwai alama ta amintaka da juna.

Sojojin Faransa sun jima suna hulda da kasashen yankin SahelHoto: abaca/picture alliance

Tuni dai masu lura da al'amuran yau da kullum irin malamin tarihi a Jamhuriyar Nijar Malam Nouradine Ibrahim ke da ra'ayin cewa, ya zama kusan tilas ga Chadin ta yi wa kanta zabi tsakanin sojojin waje da na makwabtanta kamar Nijar. Sai dai wasu kamar malami a jami'ar birnin Tahoua Atto Namaiwa a nasu tunanin korar sojojin Faransa daga kasashen Afirka da ta raina, na nuni da yadda kasashen suke ganin sojojin wata kasa kamar Faransan ba za su sadaukar da kansu domin wadannan kasashe su samu ci-gaba ba. Abun jira a gani shi ne yadda ficewar sojojin Faransa dag kasar ta Chadi zai kasance, duk da cewar babu wani wa'adi da N'Djamena ta bayar. An dai jima ana rade-radin akwai yiwuwar kasar ta Chadi ta  kasancewa mamba a kungiyar Kasashen Yankin Sahel ta da ta kunshi Nijar din da a yanzu suka kulla sabuwar hulda da Mali da kuma Burkina Faso, abin da ake ganin zai karfafa hulda tsakanin kasashen.