1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe Rasha da Ukraine za su gana

March 27, 2022

Bayan kwashe kimanin wata guda ana tafka yaki tsakanin Rasha da Ukraine, gwamnatin Kyiv ta ce za a gudanar da wata tattauna a karo na biyu tsakaninta da makwafciyarta Moscow.

Shugabannin kasashen Rasha da Ukraine
Hoto: A. Gorshkov/SPUTNIK/AFP/Getty Images/Presidency of Ukraine/AA/picture alliance

Hakan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin ta hanyar diflomasiya. Ana dai sa ran tattaunawar ta gudana a kasar Turkiyya.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na facebook, David Arakhamia da ke zama dan siyasa a Ukraine ya ce, bayan cimma wata yarjejeniya ta kafar bidiyo, tawagar bangarorin biyu za su tattauna a karo na biyu a ranakun Litinin da Talata gaba-da-gaba a kasar Turkiyya.