1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe sun halarci taron Afghanistan a Bonn

December 5, 2011

Wakilai kimanin 1000 ne daga kasashe fiye da dari da kungiyoyin duniya suke halartar taron na Afghanistan a nan Bonn, inda suka yi alkawarin zasu ci gaba da taimako da goyon bayan kasar ko bayan janye sojojin NATO.

Wakilai a zauren taron Afghanistan a BonnHoto: dapd

Burin taron shine ayi nazarin irin ci gagban da kasar ta samu, shekaru 10 bayan taro na farko da aka yi, inda jim kadan bayan kawar da gwamnatin Taliban a kasar ta Afghanistan, aka dora Hamid Karzai a matsayin shugaban gwamnatin wucin gadi a wannan kasa. Kasashen yamma na kungiyar Nato sun yi alkawarin zasu janye sojojin su daga kasar ta Afghanistan a shekara ta 2014, tare da mika al'amuran tsaro musamman a hannun yan kasar. A jawabin ta gaban wakilan, shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel tace ko bayan kwashe sojojin na kasashen yamma, Afghanistan ba za'a kyale ta taci karen ta ba babbaka ba, kasashen dake taimakon ta a yanzu, zasu ci gaba da bata gudummuwa har sai ta kai ga tsayawa kan kafafun ta.

"Tace nan da yan makonni kalilan masu zuwa, tabbatar da tsaro a misalin rabin kasar Afghanistan zai koma hannun yan kasar. Wannan dai wani sabon mataki ne wanda daga yanzu zuwa shekara ta 2014, zamu mika kasar baki dayanta a hannun yan Afghanistan. To sai dai ko bayan hakan, aikin mu bai kare ba, saboda zamu ci gaba da bada goyon baya da horad da jami'an tsaro da sanya su amatsayin da zasu iya kare kasar su da kansu. Zamu kara yawan taimakon da muke bayarwa na raya kasa, domin cimma burin da muka sanya a gabanmu. Zamu maida hankali domin ganin kasar ta sami ci gaba ta fuskar siyasa, tare da karfafa manufofi na sulhu tsakanin juna, haka nan kuma da sake gina kasar ta Afghanistan a fannin tattalin arziki."

Shugaban Afghanistan Hamid KarzaiHoto: dapd

Tun ranar Asabar shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya iso Bonn, inda ya gudanar da shawarwari da jami'ai na kungiyoyi da na kasashe, cikin su har da ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle, a game da bukatun kasar sa nan da shekaru masu zuwa da kuma irin sakamakon da yake bukatar taron na Bonn ya samu. Shugaban yace gwamnatin sa tana bakin kokarin ta a matakan yaki da cin rashawa, tana kuma samun ci gaba a kokarin tana sulhunta yan kasar baki daya, amma tana bukatar taimako da goyon baya mai yawa daga ketare.

"Ga yan Afghanistan, shekaru 10 da suka wuce zuwa yanzu, sun kawo fata mai yawa da kyakkyawar dama da kuma ci gaba ga rayuwar jama'a, irin yadda ba'a taba gani ba a tarihin wannan kasa. Mun kirkiro matakai na ci gaban siyasa, mun sami nasarar hade yan Afghanistan wuri guda, mun kuma sami nasarar tabbatarda ganin cewar Afghanistan ta sake zama kasa ga dukkanin yan Afghanistan."

Shugaban na Afghanistan wanda shi da kansa ne ya shugabanci taron na Bonn, yace kasar sa tana bukatar taimako na miiyoyi dubbai daga ketare akalla nan da wasu shekaru 10 masu zuwa, to sai dai wakilai sun maimaita cewar taron na Bonn, ba taro ne na nemarwa Afghanistan taimakon kudi ba, saboda haka babu wani alkawari na kudi da aka yiwa wannan kasa.

Shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel da ministan harkokin waje, Guido WesterwelleHoto: dapd

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle, wadda kasar sa ta karbi bakuncin taron na Afghanistan yace alhakin Jamus da na kasashen yamma kan Afghanistan ba zai kare daga shekara ta 2014 ba.

"Yace muna son aikewa da sako a fili ga yan Afghhanistan cewar ba zamu rabu daku ba, ba kuma zamu yi watsi daku ba."

Taron na kwana guda ya gudana ne ba tare da halartar Pakistan ba, wadda ake ganin tana daya daga cikin kasashen da in bata, zaman lafiya ba zai samu a kasar Afghanistan ba. Tun bayan harin jirgin saman yakin Amerika a karshen jiya, da ya kashe yan Pakistan 24, kasar tace zata kauracewa taron na Bonn, duk da kokarin da Amerika da Jamus suka yi na jan hankalin Pakistan din ta tura wakilan ta.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Yahouza Sadissou