1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kare kanta game da korafin kasashe

Zulaiha Abubakar
December 27, 2019

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana takaici game da yadda Amirka ke jinkiri wajen baiwa jami'an gwamnatin Rasha da wasu kasashen ketare izinin shiga kasar.

Österreich R20 Austrian World Summit in Wien
Hoto: Reuters/L. Niesner

Wannan jawabi dai na kunshe ne cikin sanarwar da kakakin zauren Majalisar Dinkin Duniyar ya raba wa manema labarai, jim kadan bayan mahukuntan Rasha sun soki sakataren Majalisar Dinkin Duniyar da kau da kai game da yadda Amirka ke jan kafa a wajen bayar da izinin shiga kasar. Gabanin wannan korafi, sai da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana yadda Amirka ta yi watsi da bukatar wakilanta wadanda za su ziyarci shelkwatar Majalisar Dinkin Duniyar da ke birnin New York na Amirkan, al'amarin da ma'aikatar ta nunar da cewar zai iya kara tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.