Kasashe za su tallafa wa 'yan Rohingya
October 23, 2017Talla
Kamar yadda MDD ta sanar, kasashen na duniya sun amince da hakan ne lokacin wani taron musamman da suka yi a birnin Geneva na kasar Switzerland. Taron dai ta hadin guiwa ce tsakanin kungiyar tarayyar Turai ta EU da MDD da kuma kasar Kuwet. Akwai ma wasu dala miliyan 50 din da kasashen suka amince za su samar da kayayyaki don musulmin marasa rinjaye na Myanmar.
Cikin watan Fabrairun badi ne dai za su amfana da tallafin. Kimanin 'yan Rohingyan dubu 900 ne suka tsere zuwa Bangaladash a karshen watan Agustan bana sakamakon rikici da sojin kasar Myanmar.