1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Taron sulhunta Rasha da Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
May 17, 2023

Shugabanni kasashen Zambia da Senegal da Congo da Uganda da Masar gami da Afirka ta Kudu sun nemi ganawa da Shugaba Vladmir Putin na Rasha da takwaransa Volodmyr Zelensky na Ukraine.

BRICS Treffen in Brasilien/Vladimir Putin und Cyril Ramaphosa
Hoto: Mikhail Metzel/ITAR-TASS/IMAGO

A kokarinsu na kawo karshen rikicin da kasashen Rasha da Ukraine suka kwashe sama da shekara suna yi.

Shugaba Cyril Ramaphosa wanda ya tattauna da shugabannin da ke gaba da juna ta wayar tarho, ya tabbatar da amincewarsu na shirya wani taron samar da zaman lafiya daga shugabnnin kasashen Afirka.

Taron da za a yi shi ba tare da kasancewar shugabannin biyu a zaure guda ba, Ramaphosa ya ce babban burinsu shi ne na ganin sun yi nasarar shawo kan Putin da Zelensky na maida wukakensu kube.

Afirka ta Kudu da Senegal da Congo da Uganda a shekarar da ta gabata sun kauracewa bukatar MDD na sukar mamayar Rasha ta kaddamar a Ukraine, yayin da kasashen Zambiaa da Masar da kakausar murya suka soki matakin.