Kawo karshen cutar HIV\AIDS a kan kananan yara
February 1, 2023Talla
Sabon shirin da ke da nufin inganta yadda ake gudanar da gwaji da yadda za a kula da masu dauke da cutar da ma hanyoyin kaucewa kamuwa da cutar.
Yarjejeniyar ta Dar es Salam da ta kunshi kasashen Najeriya da Angola da Kenya da Afirka ta Kudu da Uganda da Tanzaniya sun amince da kawo karshen wannan cuta a tsakanin kananan yara.
Hukumar da ke sanya idanu kan yaduwar kwayar cutar HIV AIDS ko kuma SIDA ta Majalisar Dinkin Duniya UNAIDS, ta ce kusan kaso 50 cikin dari na yaran da ke dauke da cutar ne ba sa samun magani, kuma a cikin kowane mintuna biyar a kan sami yaro daya da ke mutuwa sanadiyar wannan cuta.