Kasashen BRICS na ganawa a Indiya kan makamashi
May 14, 2026
Minitocin harkokin wajen kasashen kungiyar BRICS ciki har da Iran da Rasha na ganawa a Indiya, domin yin wata tattauna da ake sa ran za ta mayar da hankali kan batun rikicin yankin Gabas ta Tsakiya da kuma matsalar makamashi.
Tangardar da aka samu a zirga-zirgar jiragen ruwa sakamakon toshe mashigin Hormuz ta haddasa tashin farashin iskar gas da man fetur, lamarin da ya kara matsa lamba ga tattalin arzikin kasashen da suka dogara sosai kan shigo da makamashi daga waje musamman Indiya.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Indiya, Randhir Jaiswal, ya shaida wa manema labarai cewa taron na kwanaki biyu zai tattauna batutuwan duniya da na yankuna da suka shafi muradun bai baya na kungiyar.
BRICS na tsara tunkarar manufofin shugaban Amurka Trump
Sai har yanzu ba a tabbatar ko wakilan dukkan kasashen BRICS za su halarci taron na New Delhi ba, haka kuma akwai rashin tabbas kan ko taron zai fitar da sanarwar hadin gwiwa saboda sabanin ra'ayi a tsakanin membobin kungiyar, musamman dangane da rikicin Gabas ta Tsakiya.