1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Dawo da hulda da kasashe

Salissou Boukari AH
September 22, 2023

A Nijar sannu a hankali kasashen da suka dakatar da hulda da kasar saboda juyin mulkin na dawowa kan bakansu. Kasashen na dawo da hulda ne sakamakon yadda suka ce al'umma na wahala saboda rashin tallafi.

Louise Aubin jami'ar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin yammacin Afirka
Louise Aubin jami'ar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin yammacin AfirkaHoto: DW

 

Sannu a hankali dai gwamnatin da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar ta Nijar suka girka na samun karbuwaTakun saka tsakanin Nijar da Faransa a faikace ganin cewa wasu daga cikin kasashen da a baya suka dakatar da ayyukansu domin nuna adawa da juyin mulkin sun soma dawowa inda suke cewa za su ci gabada aiki ne domin al'umma kaman yadda kasar China da farko ta sanar da matsayinta. Sai dai ga masana harkokin kasa da kasa suna ganin  tun farko akwai kasashen da ba su cikin masu matsin lamba ga kasar ta Nijar, kamar yada Moutari Ousmane tsohon jami'in diflomasiyya kuma tsohon dan majalisar dokoki na Njar ya bayyana. Sai dai da yake magana daga nasa bangare Alhaji baba Elmakiyya, shugaban kungiyar farar hula ta duniya reshen Turai dan Nijar da ke zama a Nijar da kuma Faransa, ya ce daman sun san haka za ta kasance domin dole kasashe su yi hulda a tsakaninsu, amma kuma sai ya yi kira ga sabbin hukumomin na Nijar da cewa kasashen na waje irin su Faransa ya kamata ne a sake zama a yi sabuwar yarjejeniya da su don gudun komawa 'yar gidan jiya.

Faransa har yanzu ba ta amince ba da sabbin shugabanin mulkin sojoji na Nijar

Hoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

Ya zuwa yanzu dai batun ficewar sojopjin Faransa daga kasar ta Nijar shi ne akin kusan dukannin 'yan kasar wanda ake ganin dawowar da wasu kasashe ke yi sannu a hankali domin ci gaba da hulda da kasar ta Nijar tamkar masokiya ce ga shugaban kasar Faransa da ke ci gaba da nacewa a kan bakansa na cewa kasarsa ba ta yarda da sojojin da suka yi juyin mulki ba a matsin halastattaun shugabanin kasar ta Nijar ba.