1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Australia tana matsayi na hudu a lashe lambobi

Lateefa Mustapha Ja'afar SB
July 29, 2024

Mutane da dama ne suka shiga hannun jami'an tsaro a Faransa, sakamakon yunkurin kawo tsaiko a gasar guje-guje da tsalle-tsalle Olympics da ke gudana a birnin Paris. Yayin da Jamus ke jan kafa wajen lashe lambobi.

Paris 2024 | 'Yan wasa lokacin a gasar guje-guje da tsalle-tsalle Olympics
'Yan wasa lokacin a gasar guje-guje da tsalle-tsalle Olympics Hoto: Ebrahim Noroozi/AP Photo/picture alliance

Yayin da ake ci gaba da fafatawa a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a birnin Paris na kasar Faransa, ministan cikin gidan kasar Gérald Darmanin ya sanar da cewa jami'an tsaro sun cafke kimanin mutane 50 sakamakon yunkurin kawo rudani a yayin gasar. Darmanin ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na kasar na France 2, inda ya ce mutanen sun so su gudanar da zanga-zanga ta masu tsattsauran ra'ayin yayin wasannin farko na gasar. Da ma dai jaridar Le Parisien ta ruwaito cewa, an cafke mambobin masu tsattsauran ra'ayin kare muhalli da ke zanga-zanga da suka shirya kawo tarnaki a gasar ta Olympics.

Karin Bayani: Wasannin Olympics cikin tsaka mai wuya

Jami'an tsaron Faransa a gasar guje-guje da tsalle-tsalle Olympics Hoto: Straubmeier/nordphoto GmbH/picture alliance

Fadar Kremlin ta sa kafa ta yi fatali da abin da ta kira jita-jitar kafafen yada labaran Yamma da ke cewa Rasha ce ke da alhakin kai hari a layukan dogon Faransa, tana mai cewa kafafen na son su dora kowanne irin laifi ne kawai a kan Moscow. Wasu masu kokarin kawo tasgaro a gasar ne dai suka kai jerin hare-hare a layukan dogon Faransan a Jumma'ar da za a gudanar da bikin bude gasar, abin da ya janyo rudani da cunkoson matafiya tare da fito da raunin matakan tsaron da mahukuntan  Paris din suka dauka gabanin wasannin na Olympics. Tawagar 'yan wasan Australia ta kunshi 'yan wasa 80 wadanda ke karawa a wasanni 17 daga nan zuwa 11 ga watan Agusta lokacin da za a kammala gasar. A yanzu haka dai Australia na daya daga cikin wadanda ke kan gaba wajen samun lambobi.

'Yan wasan kwallo kafa lokacin a gasar guje-guje da tsalle-tsalle Olympics Hoto: Rémy Perrin/MAXPPP/dpa/picture alliance

Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na mata ta kasar Amurka ta samu nasarar kai wa wasannin kusa da na kusa da na karshe wato Quarter Finals, bayan da ta lallasa Jamus da ci hudu da daya a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsallen wato Olympics da ke gudana a yanzu haka a birnin Paris na kasar Faransa. Sai dai duk da wannan dukan kawo wukar da tawagar Amurka ta yi wa takwararta ta Jamus, mai horas da 'yan matan Amurka Emma Hayes ta bayyana cewa ba su yi wasan mai kyau ba kwata-kwata. Hayes ta ce wasa ne na fahimtar juna dole da ma za a wahala kuma 'yan wasan nata sun wahala a wasan na ranar Lahadin da ta gabata, sai dai ta bukaci da su canza salonsu a wasanni na gaba duk da cewa ta san sun fafata ne da kungiyar da ke da karfi.

'Yan China a gasar guje-guje da tsalle-tsalle Olympics Hoto: Steph Chambers/Getty Images

Chaina ke kan gaba da zinare hudu azurfa biyu da tagulla biyu, sai Japan da Koriya ta Kudu na mara mata baya a matsayi na biyu da na uku suma da zinare hudu azurfa biyu tagulla daya kowaccensu sai Australia a matsayi na dudu ita ma zinare hudu da azurfa biyu. Amurka na matsayi na biyar da zinare uku da azurfa shida da kuma tagulla uku, ita kuwa Faransa mai masaukin baki tana matsayi na shida da zinare uku azurfa uku da kuma tagula biyu kana Jamus tana matsayi na 10 ne da zinare daya tilo.

Bastian Schweinsteiger tsohon dan wasan JamusHoto: Federico Gambarini/dpa/picture alliance

Tsohon dan wasan tsakiya na Jamus Bastian Schweinsteiger na shirin bin sawun dan uwansa, na zama mai horas da 'yan wasa. Schweinsteiger ya yi murabus a matsayin dan wasan Jamus, bayan da ya lashe gasar Zakarun Turai wato Champions League a 2013 da kuma Kofin Kwallon Kafa na Duniya a shekarar da ta biyo baya, inda ya ci gaba da wasa. Mai shekaru 39 a duniya ya shaidawa mujallar wasanni ta Kicker cewa duk da ya na jin dadin yadda yake gudanar da sharhunan wasannin a gidan talabijin, yana tunanin nan ba da jimawa ba zai koma cikin kungiya domin bayar da tasa gudunmawar ta kwarewar da yake da ita a fannin tamaulan ga wasu 'yaan wasan. A yanzu dai dan uwan Bastian Schweinsteiger wato Tobias Schweinsteiger na horas da kungiyar kwallon kafa ta Osnabrück da ke Bundesliga rukuni na biyu.