Kasashen EU sun amince da sabon tsarin dakile bakin haure
December 9, 2025
Sabon tsarin ya kunshi hanzarta tasa-keyar wadanda ba su cancanci samun mafaka ba da kuma kafa asusun hadin kai da zai tara kusan euro miliyan 430 don tunkarar matsalar ta bakin haure. Kungiyar EU ta kuma tanadi sake tura mutane fiye da 21,000 zuwa kasashen kungiyar da ba su cikin matsanancin cunkoso.
Jami'an EU sun ce matakan za su taimaka wajen hanzarta tantance bukatun mafaka da mayar da wadanda ba su cika sharudda ba, musamman a kasashen Turai da suka fi fuskantar matsin lambar bakin hauren kamar Cyprus, Girka, Italiya da Spain.
Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun soki tsarin, suna ganin zai kara tsananta halin da 'yan gudun hijira ke ciki. Wasu sun kwatanta shi da tsauraran matakan da gwamnatin Amurka ta aiwatar a baya, suna gargadin cewa sabon tsarin na iya cutar da masu neman mafaka da al'ummomin da suka karbe su a cikin kasashen na EU.