1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Kasashen EU za su bai wa Ukraine rancen euro biliyan 90

December 19, 2025

Shugabannin kasashen Turai sun cimma matsaya wajen amincewa da bai wa Ukraine rancen kudi domin cike gibin da take fuskanta a kasafin kudi.

Shugaban Kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyj
Shugaban Kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyj Hoto: John Thys/AFP/Getty Images

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Antonio Costa, ya ce wannan mataki zai bai wa Ukraine damar samun kudaden da take bukata wajen kare kanta da kuma kula da muradun al'ummar kasar da ke fama da radadin yaki.

Karin bayani:Jamus ta shirya mika kadarorin Rasha da ke hannun wa Ukraine

Alhali kuwa shugaban Gwamnatin Jamus Friedrich Merz, ya yi ta kokarin ganin an yi amfani da kadarorin Rasha da aka sanya wa takunkumi a kasashen Turai wajen tallafa wa Ukraine da su. To amma ya yi rashin nasara kasancewar bai samu rinjaye daga sauran mambobin kungiyar ba.

Karin bayani:Trump: An kusa daina yakin Rasha da Ukraine

Kazalika, Shugaban Gwamnatin Jamus ya ce yana da yakinin cewar Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai fara nazari kan kawo karshen yakin cikin gaggawa dangane da kudurin da suka dauka na tallafa wa Ukraine.

Shi kuwa shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana yarjejeniyar kan tallafin Ukraine a matsayin babban ci gaba kuma "hanya mafi amfani" wajen tallafa wa Ukraine a yunkurin kare kanta daga Rasha.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW