1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSpaniya

Spaniya za ta amince da kasar Falasdinu

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 17, 2024

Firaministan Spaniya Pedro Sanchez ya bayyana cewa, zai sanar da ranar da Madrid za ta amince da zaman Falasdinu kasa mai cikakken iko a ranar Larabar makon gobe.

Spaniya | Firaminista | Pedro Sanchez | Amince wa | Kasa | Falasdinu
Firaministan Spaniya Pedro SanchezHoto: Thomas Coex/AFP

Firaministan na Spaniya Pedro Sanchez ya bayyana hakan ne, yayin da yake tattaunawa da wani gidan talabijin mai suna La Sexta mai zaman kansa a Spaniyan. Ya bayyana cewa suna tattaunawa da sauran kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU kan amince wa da kasar Falasdinun, bayan da aka tambaye shi ko zai bayyana amincewar kasarsa a ranar Talatar makon goben kamar yadda jami'in hulda da kasashen ketare na kungiyar Tarayyar Turan EU Josep Borrell ya bayyana a baya. A cewarsa yana ganin a ranar 22 ga wannan wata na Mayu da muke ciki, zai tantance hakan yayin jawabin da zai yi a gaban majalisar dokokin Spaniyan. Cikin watan Maris din wannan shekarar ne Sanchez ya sanar da cewa kasarsa da takwarorinta na kunyar EU Ireland da Sloveniya da kuma Malta, sun cimma matsaya domin yadda da kasancewar kasashe biyu a yankin na Gabas ta Tsakiya da ke fama da rikici wato kasar Falasdinu bayan Isra'ila.