SiyasaJamus
Kasashen EU sun dakatar da allurar AstraZeneca
March 15, 2021![Weltspiegel 15.03.2021 | Corona | AstraZenevca-Impfstoff](https://static.dw.com/image/56874613_800.webp)
Talla
Ministan kiwon lafiya nan Jamus Jens Spahn ya ce an dauki matakin dakatar da allurar ce bisa shawarar cibiyar Paul Ehrlich da ke sanya ido kan rigakafi a kasar. Ana dai zargin allurar na haifar da daskarewar jini a kwakkwalwar wadanda ak yi wa.
A nashi martanin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce kasarsa za ta dakatar da amfani da rigakafin har sai hukumar kula da magunguna ta Turai ta binciki allurar wala'alla a nan gaba za ta iya ci-gaba da amfani da ita. Yayin da ita ma kasar Italiya ta bi sahun kasashen.
A rahotonsa, kamfanin AstraZeneca ya ce mutane 37 kacal cikin miliyan 17 da aka yi wa rigakafin a kasashen Turai 27 da Birtaniya suka samu daskarewar jinin, a don haka babu wata kwakkwarara hujjar cewa allurar ta na da hatsari.