An kammala taron birnin Riyadh kan rikicin Gaza
November 12, 2023Shugabanni kasashen Larabawa da Musulmai a yayin taron da suka gudanar a birnin Riyadh na kasar Saudiyya sun yi Allah wadai da luguden wutar da dakarun Isra'ila ke yi wa zirin Gaza, sai dai sun gaza bayyana matakan ladabtarwa na tattalin arziki ko na diflomasiyya da ya kamata su dauka kan Isra'ilar ba.
Karin bayani: Taron kasashen Larabawa da Musulmai
A sanawar da suka fitar a karshen taron shugabanin sun yi watsi da hujjojin Isra'ila na cewa ta dauki wannan mataki ne domin ''kare kanta'', sannan kuma sun bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gaggauta daukar kuduri domin kawo karshen cin zarafin da Isra'ila ke yi wa al'ummar Falasdinu.
Karin bayani: Gaza: Yarima ben Salmane ya yi tir da hare-haren Isra'ila
A daya gefe kuma sun yi watsi da duk wata mafita ta siyasa da za a gabatar nan gaba domin magance rikicin muddin za ta shata raba zirin Gaza da Yamma da Kogin Jodan da ke karkashin mamayar Isra'ila.
Daga nasa bangare, shugaban kasar Iran Ebrahim Raissida wannan ne karon farko da ya ziyarci Saudiyya tun bayan dawo da alaka tsakanin kasashen biyu ya bukaci kasashen Musulmi da su ayyana sojojin Isras'ila a matsayin '''yan ta'adda''. Kasar Aljeriya kuwa ta shawaraci kasashen da su yanke huldar diflamasiyya da Isra'ila muddin ta ci gaba da yin fatali da kiraye-kirayen tsagaita buda wuta.