Kasashen Larabawa na nazarin alakarsu da Isra'ila
September 16, 2025
Talla
Wannan kiran ya fito ne cikin sanarwar haɗin gwiwa ta shugabannin ƙasashe kusan 60, mambobin kungiyar Ƙasashen Larabawa da ta Musulmin, bayan taron gaggawa da suka gudanar a ranar Litinin a birnin Doha na kasar Qatar.
Shugabannin sun bayyana cewa, baya ga tunanin sake fasalin huldar diflomasiyya da Isra’ila, dukkanin kasashen mambobi kamata ya yi su dauki matakan shari’a da na aiki tare don dakile Isra’ila daga ci gaba da kai hare-hare a kan Falasdinawa.
Harin Isra'ila a Doha ya tarwatsa kokarin diflomasiyyar da Qatar da Masar suka jagoranta domin kawo karshen yakin da ya dauki kusan shekaru biyu a Zirin Gaza