Kasashen Larabawa sun bukaci a kawo karshen yakin Gaza
May 16, 2024Kungiyar kasashen Larabawa ta bukaci da a kai jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dindin Duniya zuwa yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye, kafin a cimma daidaito na kafa kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci.
Sai dai da akwai wuya wannan kira ya yi tasiri, duba da sarkakiyar rikicin da aka share shekaru ana yi a wannan yanki.
Karin bayani: G20 ta amince da samar da kasar Falasdinu
A cikin sanarwar da ta biyo bayan taron da aka kammala a ranar Alhamis, shugabannin kasashen Larabawan sun bukaci a shirya babbar mahawara ta kasa da kasa a karkashin inuwar Majalisar Dindin Duniya domin kawo karshen zubar da jini a zirin Gaza da yaki ya daidaita.
Karin bayani: Majalisar Dinkin Duniya ta ce samar da kasar Falasdinu ya zama wajibi
Sai dai girke jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD a yankin Falasdinu abu ne da ke bukatar samun sahalewa daga Isra'ila, abinda wasu masana ke ganin cewa zai yi matukar wahala ko ma ba zai yiwu ba.
A daya bangaren kuma firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu ya kasance babban mai adawa da matakin kafa kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci a matsayin mafita ga rikicin yankin, duk da karbuwa da wannan shawara ke samu a gurin Amurka da wasu kasashen nahiyar Turai.