1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan kutsen Turkiyya a Libiya

Mahmud Yaya Azare ZMA
December 27, 2019

A daidai lokacin da Turkiya ke daukar matakan karshe na tura sojojinta zuwa Libiya don baiwa gwamnatin hadakar da MDD ke amincewa da halaccinta, kasashen Larabawa sun yi tir da yunkurin

Saudi Arabien König Salman bin Abdulaziz in Tunis
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Belaid

Tun a ranar  Laraba ne dai shugaban Turkiyya, Racep Erdogan ya fara daukar matakan kar-ta-kwana wajen aiwatar da yarjejeniyar tsaron da kasarsa ta cimma da Libiya. Bayan da  Libiyar a hukumance ta nemi Turkiyya data tura dakarun sojinta na sama da kasa dana ruwa, don baiwa fadar mulkin kasar Tripoli tsaro, daga hare hare ba kakkautawa da mayakan madugun 'yan tawayen kasar Janar Haftar ke kai mata da niyar kwace ikonta.

Yadda shugaban na Turkiyya ya fara aiwatar da wannan yarjejeniyarta kaiwa ziyarar ba-zata tare da tawagar jami'an leken asirin kasarsa zuwa kasar Tunusiya, inda a nan ya fito karara ya nuna aniyarsa ta tura dakarun kasarsa zuwa kasar ta Libiya:

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na TurkiyyaHoto: picture-alliance/AP Photos/Pool Presidential Press Service

'Ba zamu bar kawarmu Libiya, 'yan gada-gada da sojojin haya na ketare su ci gaba da wasa da lamuran tsaronta ba. Za mu kare halattaciyar gwamnatin hadin kan kasa da MDD ke aminta ta halaccinta daga masu kokarin juyin mulki, da ma masu taimaka musu, wadanda ke son su ga Libiya ta zauna karkashin mulkin danniya da ta'addanci. Mun lashi takobi baza mu yarda haka ya wakana ba.

Haka zalika, shugaban na Turkiyya, ya nemi Tunusiya data shiga wani kawance na kasashe uku da suka kunshi Turkiyya da Tunusiya da Aljeriya, don ganin an samu cikakken tsaro da zaman lafiya a Libiya.

A nasa bangaren, shugaban Tunusiya Qais Saeed duk da cewa bai fito karara ya nuna amincewa da shiga wannan kawancen ba, ya nuna amincewarsa da duk wani yunkurin da zai tsamar da zaman lafiya a yankin ta hanyar daukar matakan diplomasiyya.

"Muna aiki tukuru don ganin an samu daidaito tsakanin bangarori masu rikici a Libiya. Domin mun yi amanar cewa tsaron Libiya yana daga cikin tsaron Tunusiya. Muna kuma maraba da duk wani yunkurin diplomasiyya na ganin an kashe wutar yakin basasar da ke  Libiya, da samar da kwanciyar hankali da ci gaba a dukkan bangarorin rayuwa."

Shugabannin kasashen LarabawaHoto: Getty Images/AFP/Z. Souissi

 Tuni dai kungiyar kasashen Larabawa, a ta bakin Magatakardarta Ahmed Abul–Geit, ta nuna damuwarta da wannan take-taken na Turkiyya, tana mai yin Allah wadai da duk wani yunkurin kutsen sojojin kasar ta Turkiya da ma na wasu kasashen ketare cikin kasarta Libiya:

"Muna mummunar fassara da wadannan take-taken na Turkiyya. Domin mun yi amanar cewa, Turkiyya tafi fifita bukatun rajin kanta fiye dana al'ummar Larabawa. Duk wani kutsen da sojojinta zasu yi a Libiya, zai iya bude gasar tsoma bakin kasashen ketare, kuma hakan ba zai yiwa al'ummar kasar dadi ba."

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani