1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Thailand da Kambodiya sun yi sulhu

October 26, 2025

Kasashen Thailand da Kambodiya sun sanya hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta bayan sun yi wani dan karamin yakin kwanaki na kan iyaka a watan Yuli.

Kasashen Thailand da Combodia sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta
Kasashen Thailand da Combodia sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta Hoto: Mohd Rasfan/AFP/dpa/picture alliance

Shugabanin Thailand da kuma Kambodiya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita wuta bisa jagorancin shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya shiga tsakani a watan Yulin wannan shekarar domin kawo karshen rikicin kan iyaka na kwanaki biyar da ya barke tsakanin kasashen. An dai sanya hannu kan yarjejeniyar bayan da shugaba Trump ya isa taron koli na kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya a Kuala Lumpur.

Karin bayani: Thailand da Cambodiya sun zargi juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Hakan dai ya ginu ne kan yarjejeniyar da aka cimma watanni uku da suka gabata, bayan Shugaba Trump ya bukaci shugabannin kasashen biyu a wancan lokacin su kawo karshen rikicin ko kuma su yi kasadar dakatar da tattaunawar kasuwancin kasashensu da gwamnatin Washignton.