1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Siriya: Kasashen Turai na rububin ziyara

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 10, 2025

Rahotanni daga Siriya na nuni da cewa, ministan harkokin kasashen ketare na Italiya Antonio Tajani ya gana da sabon shugaban kasar Ahmed al-Sharaa a birnin Damascuss.

Italiya | Antonio Tajani | Ziyara | Siriya
Ministan harkokin waje na Italiya Antonio TajaniHoto: Claudia Greco/REUTERS

Ziyarar ta ministan harkokin kasashen ketare na Italiya Antonio Tajani na zaman ta baya-bayan nan wacce jami'an diplomasiyyar kasashen Turai ke kai wa Siriya, tun bayan kifar da gwamnatin kama-karya ta Bashar al-Assad a watan Disambar bara. Koda yake kamfanin dillancin labaran Siriyan SANA bai yi wani karin haske kan abin da Tajani da Ahmed al-Sharaa suka tattauna ba wata guda bayan jagoran kungiyar masu ikirarin jihadin ya kwace iko da fadar gwamnati ta Damascus, abin da  ya tilasta Assad tserewa zuwa Moscow.