Za a bude iyakokin cikin gida na Turai
June 15, 2020A wannan Litinin da yawa daga cikin kasashen Turai na kungiyar EU ke bude kan iyakokinsu watanni da dama bayan rufe su saboda cutar COVID-19.
Sai dai akwai bukatar ko da an bude iyakokin mutane kar su yi nisa da kasashensu a wani mataki na farfado da tattalin arzikin kasashen musamman a fannin yawon bude ido.
Faransa da ke zama kasa ta farko a wannan fanni na kira ga al'ummar ta da su yi hutunsu na rani a cikin kasar maimakon kai kudadensu wasu kasashen. A yayin da a hannu guda suke shirin fara wani shiri mai taken "A Faransa zan yi hutun rani na"
Kasar Spain ta sanar da cewar ba za ta bude iyakokinta a wannan rana ba a yayin da ta ke shirin karshe na karkabe cutar COVID-19. Birtaniya wacce dama bata rufe nata iyakokin ba bata cikin wannan shirin sai dai ta ce duk mai shiga kasarta sai ya yi makwanni biyu a kebe.