1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Kasashen Turai na shirin zaben shugaban EU

June 17, 2024

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai za su yi wani zama na musamman a Brussels babban birnin kasar Beljiyam, domin tattauna batun zaben wanda zai jagoranci kungiyar a nan gaba.

Shugabar hugabar EU, Ursula von der Leyen
Shugabar hugabar EU, Ursula von der LeyenHoto: Metodi Popow/picture alliance

Shugabar hukumar Turan ta yanzu Ursula von der Leyen, 'yar siyasar Jamus na neman goyon baya a wa'adi na biyu da take nema.

Jam'iyyarta ta European Peoples Party EPP a majalisar ta samu nasara a zaben Turai da aka kammala a baya-bayan nan.

Hakan dai na nuna alamun Ursula von der Leyen na iya kai labari a wa'adi na biyu na shekaru biyar da take son tsayawa takara.

Sai dai a bayyane take tana bukatar samun goyon baya daga wasu kungiyoyi na siyasa a majalisar.

A ranakun 27 da 28 ne dai za a gudanar da zaben na kungiyar EU duk da cewa akwai alamun samun dan takara babu hamayya.