Kasashen Turai sun kasa cimma yarjejeniya a game da nukiliyar Iran
September 13, 2006Jakadun ƙasashe biyar masu wakilcin dundundun a kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya tare da ƙasar Jamus, sun gaza cimma yarjejeniya a kan matakin da za su ɗauka dangane da burin ƙasar Iran na mallakar makamashin nukiliya. A yayin tattaunawar su wadda ta gudana a Hedikwatar hukumar ta IAEA dake birnin Vienna, ƙasashen China da Rasha sun soki tsatsauran raáyin da Amurka ta ɗauka da kuma kafewar ta a kan haka. ƙasashen biyu sun ce suna bukatar a jinkirta domin sauraron cigaban shawarwari tsakanin babban mashawarcin ƙasar Iran kan batun makamashin Ali larijani da jamiín harkokin wajen ƙungiyar tarayyar turai Javier Solana. Mr Solana na ƙoƙarin shawo kan Iran ta amince da tayin Ihsanin da aka gabatar mata na moriyar tattalin arziki dana diplomasiyya idan ta dakatar da bunƙasa makamashin ta na Uranium.