1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Turai suna ci gaba da kokarin shawo kan matsalar Euro

November 14, 2011

A bayan da Pirayim ministan Italiya, Silvio Berlusconi yayi murabus, an nada Mario Monti ya gaje shi, tare da daukar wannan mataki a Girka, an fara baiyana fatan samun nasarar shawo kan rikicin kudi a nahiyar Turai

Sabon Pirayim ministan Italiya, Mario MontiHoto: dapd

A bayan da Pirayim ministan Italiya, Silvio Berlusconi yayi murabus, an nada tsohon kwamishinan kungiyar hadin kan Turai, Mario Monti ya gaje shi, ya kuma jagoranci kasar yadda zata fita daga mumunan matsalar bashi dake kanta. Tun ranar Lahadi, shugaban kasa, Giorgio Napolitano ya baiwa Monti izinin kafa sabuwar gwamnati ta wucin gadi, kuma yau ake sa ran zai gabatar da yan majalisar ministocin sa. Wanan mataki na Italiya da irin sa da aka dauka a Girka, ana fatan zai taimaka ga sassauta matsalar bashi dake addabar nahiyar da kuma shawo kan rikicin da kudin Euro yake ciki yanzu.

A baya-bayan nan ya zama tilas ga Italiya ta rika biyan kudin ruwa mai yawa ga duk wadanda suka sayi hannayen jarin ta. Irin wannan hali da kasar ta Italiya ta shiga na biyan kudin ruwa da ya wuce kima shi ya sanya tilas kasashen Girka da Ireland da Portugal su kasance karkashin laimar taimako na musamman daga sauran kasashen Turai. To sai dai masana sun baiyana imanin cewar wannan laima ta taimako bata da girman da zata iya daukar kasar da ita ce ta ukku a jerin wadanda suka fi karfin tattalin arziki a jerin masu amfani da kudin Euro, wato Italiya. Hakan ya kai ga fahimtar cewar idan har Italiya ta rasa kudaden tafiyar da aiyukan ta na yau da kullum, shi kansa tsarin na kudin Euro zai rushe baki daya.

Pirayim Ministan wucin gadi na Girka, Loukas PapademosHoto: picture-alliance/dpa

Sai dai kuma canjin gwamnatoci da aka samu a biranen Athens da Rome yana iya kawar da tsoron samun haka din akalla na wani dan gajeren lokaci, to amma matsalar ba za'a ce an kawar da ita gaba daya ba, saboda har yanzu ana fama da tsoron ko wasu kasashen masu amfani da kudin Euro zasu talauce, su rasa kudaden tafiyar da aiyukan su na yau da kullum. A kasar Girka, mutane da yawa suna kwashe kudaden su daga bankuna, saboda tsoron cewar nan gaba kadan kasar zata koma ga amfani da takardun kudin ta na da, wato Drachme, abin da ya kai bankunan kasar su kasance cikin wani hali na kaka-ni-kayi. Hakan ya kai ga tambayar: shin me ya kamata ayi, idan har ana son tsamo rukunin kasashen masu amfani da kudin Euro daga fuskantar mummunan hadari? Masanin harkokin kudi, kuma mashawarcin gwamnati, Clemens Fuest yace:

Ni a fahimta ta, tilas ne kasashen Girka da ma Portugal a dauki wani mataki na yafe masu wani bangare na bashin dake kansu, saboda duk abubuwan da akai ta muhawara a kansu ya zuwa yanzu basu wadatar ba. Tilas ne a kara yawan bashin da za'a yafe masu, watakila misalin kashi saba'in cikin dari ko ma abin da yafi haka.

Amma yin haka, zai kara tsananta mummunan halin da bankunan kasashen suke ciki. Sai dai idan aka dauki irin wannan mataki na rage bashin dake kan kasashen dake cikin wahala, su kuma suka amince da daukar matakan gyare-gyare masu tsanani, ana iya sa ran zasu kafa sabon rushen gyara ga al'amuran su. A game da Italiya kuwa, abin da ake bukata da farko shine goyon baya da amincewar masu huldodi da ita, inji masanin tattalin arziki, Fuest na jami'ar Oxford.

Kudin Euro na kasashen TuraiHoto: dapd

Idan mutum ya dubu tsare-tsaren kudi na Italiya, yana iya ganin cewar wai daga shekara ta 2013 kasar ba zata sami gibi a kasafin kudin ta ba. Wannan hali ne da har ma yafi na Jamus kyau. To sai dai matsalar ita ce: kasuwnanin hada-hadar kudi masu yarda da wadannan alkaluma na Italiya ba.

Fuest ya bada shawarar kirkiro wata hukuma ta musamman da zata kula da kasafin kudin kasar ta Iraliya, wadda zata rika gabatar da tsarin kudaden kasar yadda yake a zahiri ba tare da an yi masa kwaskwarima ba. Daukar irin wannan mataki yana iya jan hankali da samun amincewra masu zuba jari. Duk dfa haka, Alfons Weichenrieder, na jami'ar Frankfurt yace duk ta yadda aka duba halin da Italiya dn take ciki, tiolas kasar da rage kudaden da take kashewa, saboda bunkasar tattalin arzikin da Italiya dn take samu bai kai na sauran kasashe masu amfani da kudin Euro ba. Bayan gyara ga kasafin kudin ta, tana kuma bukatar kwaskwarima a kasuwannin daukar ma'aikata. Duk da haka, kasar zata dauki shekaru masu yawa nan gaba kafin ta fara cin gajiyar duk wasu matakai na tsimi da zata dauka yanzu.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Ahmad Tijani Lawal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani