Kakabawa Rasha takunkumi a kan rikicinta da Ukraine
February 22, 2022Jamus ce kasa ta farko da ta dauki matakin dakatar da shirin bututun iskar gas na Nord Stream 2 wanda zai rinka shigo da makamashin iskar daga Rasha, shirin da dama ke shan suka.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya kakabawa wasu manyan attajiran kasar uku takunkumin karaya tatalin arziki da ma wasu bankunan kasar biyar.
A nata takunkumin, kungiyar tarayar Turai ta ce zai shafi manyan jiga-jigan gwamnatin Vladmir Putin da bankuna da ke daukar nawin ayyukan sojojin kasar gami da rage hadahadar kasar da kasashen Turai ta fannoni da dama.
A gaba a yau mahukunta a Amirka za su fidda nasu jefrin takunkumin ga Rashar.
Kasashen na yamma dai sun ce sun yi iya yinsu wajen ganin anyi amfani da diplomasiyya domin kawo karshen rikicin, amma hakarsu bata cimma ruwa a sabili da haka dole su dauki mataki.