Kasashen yamma sun yaba wa Biden
February 20, 2021Shugaba Biden a karon farko a mastayinsa na shugaban kasa ya hallarci taron al'amuran tsaro na duniya a birnin Munich wanda ya gudana ta kafar internet. Taron wanda ke gudana duk shekara, ya kan tattauna al'amuran tsaro da fasahohin zamani kana da difalmasiyar siyasa,
A jawabinsa ya tabbatar wa sauran mahalarta taron da suka hada da Shugaba Emmaneul Macron na Faransa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma Firaministan Birtaniya Boris Johnson, aniyar sake hada kai da kasashen don dawo da martabar kasar Amirka a matsayin amintacciyar jagora.
A nata jawabin shugabar gwamnatin Jamus Merkel, ta ce matakin Amirka na yanzu na komawa yarjejeniyar Paris kan sauyin yanayi da Hukumar Lafiya ta Duniya tare da farfado da yarjejeniyar nukiliya Iran, wani babban cigaba ne da matakin hada kai tsakanin kasashen. Taron tsaro na Munich ya zo ne rana guda da taron kasashe bakwai mafiya karfin arzikin masana'antu na kasashen yamma wato G/, wanda shi ma ta yanar gizo aka gudanar da shi.