1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hadakar yaki da ta'addanci

August 26, 2025

Ana kokarin bude sabon babi cikin yaki da ta'addanci a yammacin Afirka, kungiyar kasashen yankin ta sanar da sabuwar runduna ta yaki da ta'adda. Kaso 51 cikin 100 na mutanen 'yan ta'adda suka halaka a duniya na yankin.

Manyan hafsoshin sojojin Afirka ta Yamma
Manyan hafsoshin sojojin Afirka ta YammaHoto: Richard Eshun Nanaresh/AP Photo/picture alliance

 

Soja dubu 260 ne dai kungiyar gammayar ECOWAS din ta sanar domin yaki da ta‘addan dake rayuwa ta dashi mai rai guda tara a halin yanzu. Yankin kuma da yace yana shirin kisan abun da ya kai dalar Amurka miliyan dubu biyu da dari biyar, cikin neman samar da makamai da kila ma ragowa na bukatun sojan.

Karin Bayani: ECOWAS tana da kalubale a gaba

Babban aikin sabuwar rundunar dai a cewar ECOWAS din na zaman hada kai da rundunar ko-ta kwanan yankin domin ba da taimakon kayan aiki da kila ma ragowa na bukatu na kasashen yankin. Sabuwar rundunar dai tana zaman irin ta ta uku cikin yankin ko bayan rundunar hadin gwiwar tafkin Chadi da kuma rundunar G5 ta kasashen Sahel.

Captain Abdullahi Bakoji mai ritaya dai na zaman tsoho na jami'I a rundunar sojan tarayyar najeriyar, da kuma ya ce kokarin girka sabuwar rundunar na kama da kokari na shafa sabulu maimakon tunkarar matsalar da ke kama da dashi mai rai guda tara.

Manyan hafsoshin sojojin Afirka ta YammaHoto: Gerard Nartey/AFP/Getty Images

Ya zuwa yanzun dai yammacin na Afirka na zaman na kan gaba a duniya baki daya in da ake kallon karuwar zubar jini sakamakon annobar ta‘addanci. Kuma kafa sabuwa ta rundunar dai a fadar Dr Kabir Sufi da ke zaman kwarrare bisa batun siyasar yankin dai na iya dora daukacin kasashen ECOWAS zuwa sahun gaba a kokarin yaki da ta'addar.

Daga makwabta na kasashe na kawancen Sahel na Niger da Burkina faso dama kasar mali dai ana kallon karuwar kwarara ta ta'addar ya zuwa arewacin kasar Ghana dama Benin yanzu. Ko bayan rikidar tsakiyar Najeriya zuwa wani filin daga yakin na ta'adda, da kuma mafi yawansu ke zaman na Lakurawan Mali. Ya zuwa yanzun dai kasar Jamhuriyar Nijar ce kadai take halartar taron na birnin Abuja na Najeriya da ke zaman irin sa mafi girma a tsakanin hafsoshin tsaron da ke a nahiyar.

Janar Christopher Musa babban hafsan sojojin NajeriyaHoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

To sai dai kuma duk da jerin banbanci na siyasa a tsakani na kawayen Sahel da kuma kasashen ECOWAS , ana bukatar hada kai a tunanin farfesa Usman Mohammed da ke zaman kwarrare a dangantakar kasashen ECOWAS a kokarin tunkarar annobar a kai tsaye. Wata kiddidiga dai ta ce kimanin kaso 51 cikin 100 na daukacin rai da ta'addar ta kashe a duniya baki daya dai ya fito ne cikin kasashen ECOWAS. Annobar kuma da ta tilasta kauracewar 'yan mata kusan miliyan daya daga makarantu a kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.