Taron kasashen Sahel da Sahara a Masar kan tsaro
March 25, 2016Ministocin tsaro na kasashen Afirka da Larabawa 27 da kuma wasu kasashen Turai biyar da suka hada da Italiya da Faransa da Spain da Cyprus da Girka suka gudanar da taron da nufin samar da hadin guiwa tsakanin kasashen yankin a bangaren tsaro da raya kasa.
Mukaddashin ministan harkokin wajen Masar Amjad Abdul Ghaffar ya ce:
"Manufarmu ita ce karfafa matakan tattalin arziki da na tsaro, don tunkarar ta'addanci da tsatstsauran ra'ayi da fataucin makamai da safarar mutane gami da aikata miyagun laifuffuka ta hanyar ratsa kasashenmu."
Da yake nasa tsokacin ministan tsaron Spain Pedro de Morenés ya bayyana cewa, matsalar tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a yankin na Sahel da Sahara kai tsaye sukan shafi kasashen Turai, don hakan ne ma ya sa kasashen na Turai suka mai da hankali sosai kan harkokin tsaron yankin na Sahel. Za kuma su ci gaba da ba da goyon baya ga kasashen yankin don karfafa tsaron iyakoki da kawar da kalubalen da ke da alaka da hakan.
Kwararru kan tsaro dai sun nuna muhimmancin sanya batun raya kasa a yunkurin da ake na yaki da ta'addanci da tabbatar da dawwamammen tsaro a yankin a ta bakin Mahmud Khalaf, kwararre kan dabarun warware rikice-rikice:
"Kasashen Afirka, Allah Ya albarkacemu da dumbin arzikin kasa da na mutane, amma mun kasa cin moriyarsu.Su kansu kasashen Turai da suka taba cin moriyar gangar Afirka kana suka yi watsi da ita, a yanzu sun fahimci cewa tsaron kasashen Afirka shi ne tsaronsu. Ba bu kuma ta yadda za a sami tsaro a Afirka ta hanyar amfani da karfi kadai, dole ne sai an hada da kafa wasu cibiyoyin bunkasa rayuwar matasan yankin da talauci ya yi wa katutu, ganin cewa da su ne ake amfani wajen ta da zaune tsaye da zama sojojin haya a wajen kungiyoyin miyagu da na 'yan ta'adda."
Shugaban kungiyar kasashen na Sahel da Sahara dai Ibrahim Sani Abani ya ce ministocin tsaron kasashen za su ci gaba da tattauna yiwuwar kafa wani kwamiti na musamman da zai dinga yin rigafin rikice-rikice a yankin ko shiga tsakani don sasantawa.