1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin Intanet a kasuwanci lokacin Corona

June 2, 2020

Hanyoyin sadarwar zamani na Intanet sun yi tasiri sosai wajen rage gibin kasuwanci a tsakanin 'yan kasuwar Kano da abokanin huldar kasuwancinsu a lokacin matakin kulle na Coronavirus.

Indiens Einsatz in Afrika Airtel Logo in Abuja Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Daya daga cikin dubarun hanyoyin ciniki na zamani da ‘yan kasuwar jihar Kano suka bullo da su a lokacin da ake tsaka da dokar zaman gida ta Coronavirus, ita ce ta kasuwanci da abokan ciniki ko ta waya ko ta internet. Wannan ya taimaka wajen rage gibin kasuwanci musamman da abokan ciniki na nasa.


Ko da yake tsarin ciniki ta hanyoyin sadarwar zamani ba bako ba ne ga ‘yan kasuwar jihar Kano da dama, amma kadan ne daga cikinsu suka farga da amfaninsa a lokacin da aka rufe kasuwannin jihar don katse hanzarin yaduwar cutar Covid 19.Alhaji Ali Dan Bagadaza shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Sabon Gari y ana daga cikin wadanda suka farga tun da wuri da wannan tsari:


“Ga kaya nan kana kallo, samfura. Wallahi cinikin da nake yi yanzu a gidana na tura ta hanyar zamani wallahi a Kasuwar Sabon Gari bana yi. Waya ce za mu dauki hoton takalmin mu tura wa kwastomominmu, ga irin kayayyaki da muka samu sababbi ga irin wannan ga irin wannan kuma Naira dari Naira dari biyu shi ne ribarmu. Muke musu waya su zabi wanda suke so, su aiko mana da irin da wannan da wannan  a yi lissafin kudi kaza kenan.”

Hoto: DW/J.P. Scholz


 Alhaji Ali mai shagon takalma na daga cikin 'yan kasuwar da sai a yanzu ne suka farga da tasirin kasuwanci ta hanyoyin sadarwa na zamani.
To sai dai ba duka ‘yan kasuwar ne irin wannan tunani ya zo musu ba duk da cewa suna sane da irin wannan tsarin ciniki. Alhaji Ibrahim Danyaro shugaban kungiyar manyan dilolin manyan ‘yan kasuwar Singer yana ganin rashin wuraren ajiyar kaya a kusa shi ne babban tarnaki:


“Su kasuwannin da suke a rufe yanzu, idan kana da dama ka yi ciniki ta waya ko ta internet ko ta hanyoyin kafar sadarwa, to ai ba ka da damar ka je ka bude store ka ba da kayan domin store dinka a rufe yake. Tun da kasuwanni suke a rufe, ka ga amfanin wancan ma babu shi ke nan.”


 Ga ‘yan kasuwar da suka yi muwafukar komawa wannan tsarin kasuwanci  na gani a nesa ciniki ma a nesa ko yaya suke tallata hajar tasu har ciniki ya kullu?

Hoto: DW/J.P. Scholz


“Yara ne za su dauki hoton takalmin iri kaza iri kaza sai su tura wa customer sai ya zabi  wanda yake so adadin guda kaza ne.Wasu ya ce wannan shida wannan shida, wannan carton wannan carton ,haka za a fadi jumullar kudinka kaza ne. Akwai mutumin  da ya sayi  kayan miliyan daya da dubu dari uku ina gida ina zaune aka zaba aka kai masa kuma ya biya.”


 A yanzu dai wannan tsari na kasuwancin zamani ya kawo sauki  ta hanyoyi  da dama tsakanin mai saye da mai sayarwa wanda a cewar Alhaji Ibrahim Dan Yaro dora shi a kan ginshiki na gaskiya da amana ne ya sa ake ganin nasararsa:


“Mutum ya shekara biyar goma kana hulda da shi ba ka taba ganinsa ba sai a wannan kasuwancin sai dai ka ji muryarsa ka gane shi. Amma zai aiko ma da kudi ka aika masa da kaya. Ko ka bi shi bashi ko ya bi ka haka. Amana ce ta tafi da mu.”


 Har yanzu kuwa akwai dama ta jarraba wannan tsarin kasuwanci tsakanin ‘yan kasuwar Kano da abokan cinikinsu.