1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hagia Sophia na kan hanyar zama massalaci a Turkiyya

Abdoulaye Mamane Amadou
July 10, 2020

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce za a sake matsayin katafaren wurin yawon bude idon nan Hagia Sophia zuwa wurin ibadar musulmi bayan da wata kotu ta karya matsayin wurin da yake da shi tun a shekarar 1934.

Türkei Gericht ebnet Weg zur Umwandlung der Hagia Sophia
Hoto: Reuters/M. Sezer

Wasu kungiyoyi da dama ne a kasar Turkiyya suka shigar da kara a gaban kotu, suna masu kalubalantar hukuncin shuwagabannin kasar na wancan lokaci karkashin jagorancin Mustafa Kemal, na mayar da wurin a matsayin gidan kallo da tarihi a 1934, shekaru bayan ya yi zama a matsayin wurin ibadar musulmi a yayin mulkin daular Ottomans a 1453.

Hagia Sophia ko Sainte-Sophie dai, na daga cikin wuraren tarihin da ke karkashin kulawar hukumar ilimi da raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, kana kuma ko a shekarar bara kawai akalla mutum fiye da miliyan 3.8 ne suka ziyarci wurin.