Kataloniya: Tsugune ba ta kare ba
October 6, 2017Talla
Gwamnatin 'yan aware na Kataloniya ta ce al'ummar yankin ta ka'da kuri'ar amincewa da samun yancin kai da kishi 90 ciki dari na kuri'un da aka ka'da a zaben raba gardamar da aka yi ran daya ga watan Oktoba. A ranar Talata dai mai zuwa aka shirya jagoran 'yan aware Carles Puigdemont zai jawabi. Amma kuma gwamnatin Spain ta ce Kataloniya za ta ci gaba da kasancewa cikin Spain