Katsewar hulɗar Iran da Holland
January 30, 2011Talla
Gwamnatin ƙasar Holland ta katse hulɗa tsakaninta da Iran bayan da jamhuriyar ta Islama ta zartar da hukuncin kisa ga wata mata 'yan asalinta mai riƙe da fasfo na Holland bisa laifin fataucin fodar iblis wato cocaine zuwa wannan ƙasa . Ministan harkokin wajen Holland, Uri Roesental ya kira zartar da hukuncin kisa akan Zahra Bahrami mai shekaru 46 da haifuwa tamkar ɗanya da azzaluman gwamnati ta aikata. Bahrami dai na daga cikin waɗanda suka bayyanar ga kyamarsu ga gwamnatin Iran. A shekarar 2009 ne aka kame ta bayan da ta shiga zanga-zangar nuna adawa da sake zaɓar Shugaba Mahmud Ahmadnejad .
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman