1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: An yi zanga-zanga saboda tsaro

Ahmed Salisu
August 6, 2020

Wasu matasa a karamar hukumar Dutsin Ma da ke jihar Katsina a arewacin Nigeria sun gudanar da zanga-zanga sakamakon hare-hare da 'yan bindiga ke kai musu inda su kan hallaka mutane tare da kwashe dukiyoyinsu.

Nigeria Katsina Sicherheit
Hoto: DW/H. Y. Jibiya

A hirarsa da DW, wani matashi mai suna Tasi'u Ibrahim da ke cikin wadanda suka yi wannan zanga-zanga, ya ce halin da kauyukansu suka shiga ne ya sanya suka harzuka har ma suka kai ga yin bore don jan hankalin hukumomi.

Wakilin DW a Katsina Yusuf Ibrahiim Jargaba da ke bibiyar wannan batun ya ce masu zanga-zangar sun rufe hanyar da ta hada Katsina da Kankara zuwa jahohin Kaduna da Zamfara amma daga bisani jami'an tsaro sun lallashesu, inda aka bude hanyar har ma matafiya suka cigaba da wucewa.

Jihar Katsina, wadda ita ce mahaifar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dai na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da matsalar tsaro ta yi wa daurin gwarmai.