1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai sana'ar gini a Katsina

July 3, 2019

Wani matashi a Jihar Katsina da ya kammala karatun NCE babu aikin yi, ya kama sana'ar ginin gidaje, matashin yakan kwaba siminti ya dauki bulo da kansa ya dora domin gina gida ko shago.

Nigeria energieeffizientes Haus eco@africa
Wannan wani tsohon hoto ne muka yi amfani da shiHoto: DW

 

Wannan matashi Bishir Halilu Karfi dalilin wannan sana'a ta gina gidaje ya kara fadada karatunsa har matakin jami'a inda yanzu haka ya kammala karatunsa ba digree a jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina kuma ya kara rike sana'ar kamar yadda ya yi wa DW karin makasudun kama sana'ar ginin: "Abin da ya ba ni kwarin gwiwar kama wannan sana'ar shi ne yanayin yada na ga kasar ko mutum ya yi karatun ba lallai ba ne a ce ya samu aiki kai tsaye shi ya sa na yi tinanin in kama wannan sana'ar. Matashin yana yin aiki ne tare da wasu matasan wadanda suka samu aikin yi tare da shi, da sannu-sannu da juriya ake cimma gaci kan abin da aka sa gaba kamar yadda wannan matashi Bishir ya cimma burunsa.