Sulhu da 'yan bindiga ne mafitar Katsina?
September 15, 2025
Shugabannin kanan hukumomin na jihar Katsina da ke Tarayyar Najeriya dai, na ganin matakin yin sulhu da 'yan binidgar zai kawo karshen halaka mutane da suke yi ba dare ba rana. Karamar hukumar Faskari ita ce ta baya-bayan nan wajan yin sulhun, kuma karamar hukumar Jibiya da ke jihar ta Katsinan ce ta farko da ta fara yin sasanci da 'yan bindigar. Wannan ya sa ta zama abun koyi ga sauran kananan hukumomin, kamar yadda shugabanta Surajo Ado ke cewa: "Mu a matsayinmu na shugabannin kananan hukumomi, al'ummarmu suka shiga gaba sukace kuzo mu yi sasanci....."
Yadda ake aiwatar da yarjejeniyar sulhu
A duk karamar hukumar da aka gudanar da sulhu a kan hadu a yi taro tsakanin al'ummar gari da shugabannin da kuma 'yan bindigar manya da kanana. Ado Aleru na daga cikin shugabannin 'yan bindigar dajin da suka jagoranci sulhun a Faskari, kuma ya bayar da tabbacin zaman lafiya bayan sulhun: "Wannan sasanci tin da ake yi jama'a ba su taba haduwa kamar wannan ba, shi ne yasa nake da tabbacin cewa wannan sasancin ya dore ba a Faskari ba a jihar Katsina ba ki daya."
'Yan bindigar sun saba kama makudan kudade da suke ansa daga al'umma a matsayin kudin fansa, abin da ya sa mutane ke jefa ayar tambaya kan ina za su rika samun kudin yanzu bayan anyi sulhun?
Wanne matakin gwamnatin jiha ke dauka?
Gwamnan jihar ta Katsina Malam Dikko Radda dai, ya sha alwashin taimakawa dukkanin bangarorin biyu kamar yadda yake cewa: "Wuraren da a kai sulhun nan gwamnati na nan ta shirya sa kudi masu dama, na ganin cewa da wanda aka tozarta da wanda ya amince ya rungumin sulhun duk an tallafa musu."
Wasu daga cikin gwamnatocin baya dai a jahohin Arewa maso Yammacin Najeriyar, sun yi sulhu da 'yan bindigar amma daga bisani ya lalace.