1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaurace wa masoya saboda hidimar Sallah

Ibrahima Yakubu/ MNAJuly 15, 2015

'Yan mata a Najeriya na kokawa bisa yadda samarinsu ke kaurace masu baki daya, saboda gudun daukar nauyin wasu bukatun 'yan matan a lokacin bikin Sallah.

junge Frauen mit Kopftüchern
Hoto: picture-alliance/dpa

Yanzu haka dai samari da yawan gaske a Najeriya sun tsere tare kuma da kaurace wa 'yan matansu dai-dai lokacin bikin karamar Sallah ke gabatowa, sabili da yanayin matsin tattalin arzikin kasar wajen kasa daukar dawainiyar kulawa da 'yan matansu. Wannan lamarin na nuni da yadda suka dakatar da duk wata hulda ko ziyarar masoyan nasu har sai bayan bikin Sallah, domin gudun jin kunya da fargabar sayayyar kayayyakin shagulgulan bikin Sallar.

A jihohin arewacin Najeriya dai daukar dawainiyar dinke-dinke da saye-sayen kayan kwalliya lokacin bikin Sallah na zama tamkar wata alada ga samarin Hausa, inda suke kashe wa 'yan matan nasu makudan kudade saboda bikin Sallah da kuma zuwa yawon sallah da ziyarce-ziyarce.

Bukatun 'yan matan sun fi karfin samari

To sai dai a wannan karon matsaloli da dama sun sanya samari kaurace wa 'yan matan nasu, saboda a cewar su bukatocin matan sun yi yawa.

Cincirindon sayan kayan SallahHoto: UNI

Gimbiya Maimunatu Mohammad nuna bacin ranta ne ta yi bisa ga yadda samarinta su 3 suka janye jiki daga zuwa wurinta yayin gabatowar bikin Sallah ina da ta ce:

"Ina da samari guda 3, amma dai abun mamaki a nan shi ne dukkaninsu sun kaurace min, kuma a cikin su akwai wanda na fi sonshi, shi ne ma wanda ya fi daukar alkawarin dinka min kayayyakin Sallah. A karshe dai na gane cewa yaudara ce kawai suke yi. Amma ina mai tabbatar maka da cewa duk wani daga cikin su dake tunanin dawowa bayan bikin Sallah, yana bata lokacinsa ne, domin tsere min da suka yi a wannan lokacin na nuni da cewa sam-sam ba za su iya kulawa da ni ba."

Ita ma dai wannan Gimbiyar da ta ba da sunanta da Faiza Mohammad Inuwa, fitowa ta yi karara ta na cewa lallai dai kam duk wani saurayinta da ya tsere mata a wannan lokacin, to kada mai yayi tunani dawowa Sallah, domin kowa bai da wani tasiri a rayuwarta.

"Na riga na fadi kuma zan kara nanatawa da cewa duk wani saurayi na da ya gudu a wannan lokaci, kada ma dai yayi wani tunanin dawowa bayan bikin Sallar, domin guduwar na nuna gazawarsa a kan bayar da cikakkiyar kulawa da ni, kamar dai yadda ya kamata. A wannan lokacin ina mai matukar bukatar duk wani tallafi daga masoyina, wanda ya nuna yana sona, shi ne na ke tare da shi, kuma wannan shi ne lokacin da ya kamata duk wani masoyinka ya nuna maka cewa yana sonka ta hanyar yo maka kayayyakin Sallah."

Matsin tattalin arziki ya shafi zamantakewa


A bisa dukkan alamu dai tsananin bakar talauci da fatara da rashin aikin yi da ke addabar matasa, su ne dai babban dalilin da ke sanya samarin dakatar da duk wata hulda da 'yan matan nasu.

Aikin ibada kusan karshen watan RamadanHoto: picture-alliance/AA/M. Elshamy

To sai dai ba duka aka zamo daya ba domin kuwa a cewar Amina Sanusi wata kyakkyawar matashiya a Kaduna, matsalar rashin fahimtar juna tsakanin samari da 'yan matansu, shi ne ke janyo wadannan matsaloli na goge-gogen samari lokacin duk wani biki:

"Wani cewa yake yi na bada ke jingina, sai bayan azumi. Wani kuwa janye jikinsa ne yake yi kwata-kwata. To sai dai a gani na duk wannan lamari ne da ya kamata a ce masoyan su fahimci juna, domin muddin akwai matsalar fahimtar juna, to fa babu yadda za a sami cikakken hadin kai tsakaninsu. Ni ba kudin masoyi na ba ne na ke so, ni shi kansa ne na ke so, kuma akwai ko babu muna tare. Yin hakan shi ne zai kara hada kanmu wuri daya, domin warware matsalolin da ke a tsakanin mu."

Duk da cewa soyayya da dama na mutuwa tsakanin samari da 'yan mata bayan bikin Sallah saboda yaudarar da matan ke ganin masoyan nasu na yi musu. Wasu 'yan matan dai na gafarta wa samarin nasu, yayinda wasu ke nuna turjiyarsu ga dorewar ci-gaban wannan soyayyar.


Su kuwa kungiyoyin kare hakkin dan Adam kira ne suka yi ga hukumomi da kungiyoyi da attajirai da su taimaka wajen yaye wa matasa tsananin talaucin da ke addabarsu da kuma tallafa wa samari da 'yan mata da ke bukatar kudaden sadaki don yin aure.