Kawance tsakanin Jamus da Faransa
May 15, 2012Ba da dadewa bane shugabanin Faransa da Jamus wato Nicolas Sarkozy da Angela Merkel suka kulla wata dangantaka ta kut da kut, dan ganin sun shawo kan rikicin kudin Turai, sun kuma tsamo nahiyar gaba daya daga matsalar bashin da ta shiga, to sai dai yanzu wannan zamani ya wuce kasancewar Nicolas Sarkozy bai yi nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar ba. To ko shin akwai yiwuwar ganin irin wannan dangataka ta Sarkozy da Merkel bayan sabon shugaba kasa Francois Hollande ya hau kujerar mulkin Faransa?
"Merkozy" ya zama tarihi
A zamanin Sarkozy duk sadda ake kwatanta dangantakar Faransa da Jamus, sai a hada sunayen shugabanin biyu a ce "Merkozy" tambayar da ke bakin 'yan siyasa yanzu ita ce ko shin dangantakar zata dore har a kaiga kiran shugabanin biyu "Merkollande"?
Hada sunaye irin haka ba sabon abu bane lokacin da tsohon shugaban Faransa a karkashin inuwar jamiyyar 'yan Socialist wato Francois Mitterand ke mulki ya goyi bayan shugaban gwamnatin Jamus na wancan lokacin daga jamiyyar SPD wato Helmut Schmidt dangane da shawarar da kungiyar kawancen NATO ta yanke a shekarar 1979 na marawa yarjejeniyar Warsaw baya da aika mata da makamai. Kuma a lokacin 'yan jarida sun rika masu lakabi da "Schmitterand" saboda wannan alaka da ke tsakaninsu.
Duk da haka dai, shugabanin gwamnatoci sukan hada kai su yi aiki tare ko da akidun siyasarsu sun banbanta, kuma wannan na nuna cewa banbancin da ke tsakanin Jamus da Faransa zai zama wani abun da zai kawo cigaba ga yunkurin hadin kan Turai kamar yadda Claire Demesmay wacce ke wakiltar kungiyar da ke kula da manufofin wajen kasashen Faransa da Jamus da ke birnin Berlin
"Muna aiki da kyaau tare saboda muna wakiltan ra'ayoyi daban-daban, kuma ta haka muna iya wakiltan duk ra'ayoyin kasashen da ke kungiyar tarayyar Turai, Jamus da Faransa sun cimma matsaya ta yadda kasashen Turai zasu yi aiki tare koma wani bambanci ke tsakaninsu"
Rawar Jamus da Faransa wajen tabbatar da hadin kan Turai
Abun da ya fi mahimmanci shine a cimma matsaya a cewar masanar kimiyyar, domin banda haka, abubuwa kadan ne ke da kama tsakanin masu ra'ayin mazan jiya na Faransa da Jamus, da ma 'yan Socialist din kasashen biyu. Kawancen Jamus da Faransa shine ginshikin tabbatar da cudanya da fahimtar juna a tsakanin kasanshen Turai kamar yadda Robert Schuman, tun a shekarar 1950 tsohon ministan harkokin wajen Faransa, wanda kuma ya zama shugaban majalisar dokokin Turai na farko ya bayyana. Claire Demesmay daga Berlin ta yi karin bayani
"Idan mutun ya yi misali da babban bankin Turai, 'yan Socialist wato Francois Holland da abokansa na Socilaist suna sa ran cewa bankin zata taka wata rawa daban wato kamar su bada rance ba ga bankuna kadai ba, amma kuma irin wannan mataki 'yan jamiyyar Socialist a Jamus ba zata taba amincewa da shi ba"
Yarjeniyoyi tsakanin kasashen biyu na da dogon tarihi
Daga farkon shekarar 1963 shugabanin kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Elysee wanda ya zama tamkar shinfida ga hadin kan kasashen biyu wajen yin ayyuka musamman a siyasar wajen gida da ta tsaro, kamar yadda muke gani a siyasar Turai gaba daya. wata kwakwarar manufa kuma da suke da ita, ita ce ayyukan matasa da kuma da siyasa a fanin al'adu
A lokacin de Gaulle da Adenauer sun sulhunta bambance-bambancen da ke tsakanin kasashen biyu, wanda ya zama tubalin hadin kan kasashen biyu daga bisani kuma Turai wannan na da mahimmanci sosai
An girka Kungiyar Tarayyar Turai ne da yarjejeniyar Maastricht wacce aka rattabawa hannu a shekarar 1992 haka nan kuma a zamanin Francois Mitterand na Faransa da Helmut Kohl na Jamus aka kulla ta Elysee wanda ya tanadi aiki tare da tabbatar da tsaron kasashen biyu, tun a shekarar 1988 Majalisun tsaron kasashen biyu ke ganawa bayan ko wani rabin shekara. Kwararriya kan harkokin Faransa Claire Demesmay ta ce tun a baya shugabanin Faransa da Jamus suke kulla dangantaka tsakaninsu musamman ma dan ci-gabansu kuma bisa dukkan alamu hakan zai cigaba da dorewa.
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Saleh Umar Saleh