1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin hadakar Jamus na girgidi

Suleiman Babayo LMJ
July 2, 2018

Ana ci gaba da samun takun saka tsakanin jam'iyyun CDU da CSU na Jamus wanda suka dade suna kawance da juna, kan matakan shige da fice domin kawo karshen zaman bakin haure.

Deutschland Koalitionsgespräche 2017 | Angela Merkel & Horst Seehofer
Tsamin dangantakar Merkel da SeehoferHoto: Imago/Ipon

Jam'iyyun na CDU da CSU dai sun sake komawa kan teburin tataunawa, inda ministan ciki gida na Jamus Horst Seehofer ya bayyana wa manema labarai cewa ya mika takardar murabus ga sauran mambobin jam'iyyarsa ta CSU wadanda suka yi taro a karshen mako. Wannan dai ya biyo bayan zaman tankiya da ke ruruwa tsakaninsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan kare iyakokin kasar da kawo karshen zaman bakin haure marasa takardu. Seehofer ya ce a shirye yake ya ajiye shugabancin jam'iyyar CSU da mukamin ministan cikin gida lokacin taron jam'iyyar domin neman amincewa da daftarin Tarayyar Turai kan batun bakin haure. Shi dai ministan cikin gidan Seehofer ya bayyana shirin murabus daga jagorancin jam'iyyar da mukamun minista muddun aka gaza samun mafita kan wannan batu na samun mataki kan dakile kwararar bakin haura a Jamus.

Ministan cikin gidan Jamus kana shugaban jam'iyyar CSU Horst SeehoferHoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Ita ma jam'iyyar CDU ta yi taro domin duba yanayin da ake ciki tare da neman matakan da suka dace bisa hanyoyin ci gaba da hadaka da jam'iyyar CSU mai mulki a Jihar Bavariya. Ita ma dai shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bukaci samun taka tsantsan maimakon gaba gadi daga kowanne bangare tana mai cewa:

Kauce wa matakin kashin kai

"Ina son ganin jam'iyyun CDU da CSU sun yi aiki tare, saboda muna samun nasara a Jamus, kuma muna da karfi tare. Sannan mutane suna da karfin gwiwa kanmu shi ya saka muke wannan tattaunawa. A wajena yana da muhimanci mu cire tunanin daukar mataki na kashin kai, da rashin adalcin da za a takura wani."

Shugabar gwamnatin Jamus kana shugabar jam'iyyar CDU Angela MerkelHoto: Getty Images/S. Gallup

Merkel ta kara da cewa ta fahimci koken da ake nunawa kan yadda 'yan gudun hijira suke fita daga kasar da suka fara isa wajen shiga wasu kasashen ba tare da an dauki wani mataki ba, abin da ta ce an samu fahimta ta siyasa a kai domin warwarewa. Duk da wannan neman mafita daga jam'iyyar CDU da shugabar gwamnati Angela Merkel ke jagoranta, shi dai Horst Seehofer ya shaida wa manema labarai cewa lokaci kadai zai zama alkali, domin duk wani abu na gaba ya danganta daga tattaunawar da aka cimma, inda ya ce cikin kwanaki uku masu zuwa tattaunawar da ake yi da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel za ta tantance makomarsa a siyasance.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani