1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jam'iyyun CDU/CSU na kan gaba a zaben EU

June 9, 2024

Sakamakon da ya fito ya nuna hadakar jam'iyyun shugaban gwamnatin Jamus, ba su yi abin a zo a gani ba. Hadakar jam'iyyun dai sun hada ne da SPD ta Olaf Scholz din da ta masu rajin kare muhalli da ke da kashi 14%.

Wata mai kada kuri'a a zaben majalisar dokokin EU
Wata mai kada kuri'a a zaben majalisar dokokin EUHoto: DELPHINE MAYEUR/AFP/Getty Images

Sakamakon farko na zaben majalisar Turai, na nuna cewa kawance jam'iyyun CDU/CSU a Jamus na kan gaba a fafatawar da ake yi na zaben majalisar dokokin Turan da kimanin kashi 30%.

Jam'iyyar AfD ta masu akidar kyamar baki kuwa ta kasance ta biyu da kashi 16% a zaben da aka yi a Jamus din. Sakamkon dai ya nuna hadakar jam'iyyun shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ba su yi abin a zo a gani ba.

Kimanin Jamusawa milyan 360 ne za su kada kuri'unsu a zaben, wanda ke kasancewa zaben gama-gari na farko da 'yan kasar za su zabi mambobin majalisar dokoki baya ga zaben 2021 da 2025 da ke tafe.

Karin bayani: Jamus: CDU ta sami karin tagomashi bayan zaben jihar Saxony-Anhalt 

Alkaluman farko na nuna jam'iyyar Shugaban gwamnatin Jamus Scholz SPD ta samu kaso 15 cikin 100, kasa da kashi 25.7 cikin 100 da jam'iyyar ta samu a zaben 'yan majalisar dokokin kasar a 2021. Lamarin dai bai yi wa kawancen jam'iyyun da ke tare da jam'iyyar SPD ta Mr. Scholz dadi ba. A jamlace kawancen jam'iyyun da suka hada da jam'iyyar the Greens da liberal Free Democrats (FDP), sun sama kashi 35%.

Karin bayani: Zanga-zangar kin jinin jam'iyyar AFD mai kyamar baki a Jamus 

A bangaren adawa kawancen jam'iyyun CDU da CSU sun yi samu gagarumar rinjaye da yawan kuri'u da ya kai kashi  30% a zaben EU, yayinda jam'iyyar AfD da ke kasancewa ta biyu a da'irar siyasar Jamus ta samu kashi 14%.