Japan za ta taimakawa cigaban Afirka
August 28, 2019Shugabannin Afirka da dama ciki har da shugaban kungiyar ECOWAS kana shugaban Jamhuriyar Nijar Muhamadou Issoufou da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da sauran shugabannin Afirka ne ke halartar taron na TICAD na bana wanda shi ne karo na bakwai. Taron wanda ake yinsa tsakanin kasashen na Afirka da Japan da ban hannun kungiyoyi da hukumomi da ke aiki wajen cigaban kasashe a duniya kan mayar da hankalinsa ne kacokam wajen lalubo hanyoyin da za a ciyar da nahiyar Afirka gaba da kuma kore matsalolin da suka yi mata daurin gwarmai.
Firaministan Japan Shinzo da ke zaman mai masaukin baki ya ce domin ganin kwaliya ta biya kudin sabulu, ya kamata a yi dukannin mai yiwuwa wajen duba batun sauyin yanayi da samar da cigaba ta fuskar kimiyya don ganin nahiyar Afirka ta yi gogayya da sauran takwarorinta. Baya ga wannan batu ya kuma nuna bukatar da ke akwai wajen sanya jari sosai a nahiyar, wannan ne ma ya sanya yace kasarsa za ta bada nata kason don ganin an cimma nasarar da aka sanya a gaba.
Firaminista Abe yace gwamnatin Japan zata yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an zuba jari na dalar Amirka biliyan 20 cikin tsukin shekaru uku a nahiyar Afirka domin tallafa wa nahiyar wajen samun cigaba mai ma'ana.
Da yake tsokaci kan taron na TICAD da ma kokarin Japan wajen zuba jari a Afirka, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace wannan kawance tsakanin Japan da Afirka da aka somo shi shekaru bakwai da suka gabata ya taimaka wa nahiyar matuka gaya ta fannoni da dama ciki kuwa har da batun kiwon lafiya da tsaro da ake fama da karancinsu a wasu kasashen nahiyar Afirka.
Shi kuwa shugaban kungiyar AU Musa al-Faki a nasa bangaren cewa ya yi kawancen TICAD da ban hannun Majalisar Dinkin Duniya sun taimaka wajen samarwa Afirka abokan hulda na gari, abokan da manazarta da dama ke ganin zasu taimakawa nahiyar wajen tabbatar da mafarkinta na kasancewa mai karfin fada a ji ta fuskoki da dama ciki kuwa har da kasuwanci.
Kokarin da Japan ke yi kan wannan kawance na TICAD abin a yaba ne. Ina jinjinawa kokarin MDD da Bankin Duniya da sauran masu ruwa da tsaki daga sassan duniya daban-daban. TICAD ta taimaka wajen gina kawance mai karfin gaske tsakanin Afirka da Japan da sauran abokan arziki.
Jama'a da dama a nahiyar Afirka da kwararru na zuba idanu kan irin abubuwan da nahiyar zata a amfana daga taron na wannan karon.