Kawancen tashar DW da Channels TV a Najeriya
April 18, 2016Shi dai wannan shiri za a rika gabatar da shi sau daya a kowanne mako wanda zai rika duba sabbin dabaru da suka danganci alkinta muhalli. Za kuma a rika duba batutuwan ne a nahiyar Turai da kuma yadda suke a nahiyar Afirka. Har wa yau shirin zai duba hanyoyin da za a bi wajen magance gurbata muhalli wanda hakan ke taimakawa wajen jawo dumamar yanayi.
A wani jawabi da ya yi lokacin kaddamar da shirin a Abuja, shugaban tashar DW Peter Limbourg ya ce wannan sabon shirin zai bada dama ta bankado matsalolin da muhalli ke fama da su da nufin magance su. Limbourg ya ce wannan mastayi da aka kai wani babban abin alfahari ne ga tashar DW.
A nasa jawabin, shugaban gidan talabijin na Channels TV John Momoh ya ce ya na fatan irin tsarin da shirin ke da shi zai taimaka wajen kare muhalli a nahiyar Afirka kuma suna alfahari da wannan kawance da tasharsu ta samu nasarar yi da tashar DW.
Ministar muhalli ta Najeriya Amina Mohammed ta jinjinawa wannan hadin gwiwa da tashoshin biyu suka yi wadda aka amince da ita cikin watan Disambar da ya gabata, inda ta kara da cewar hadakar ta zo a daidai lokacin da ake bukata domin Najeriya na daya daga cikin kasashen da matsalar dumamar yanayi ke shafa.